John 18

An Kama Yesu

1Da ya gama adduʼa, sai Yesu ya fita tare da almajiransa suka haye Kwarin Kidron. A wancan ƙetaren kuwa akwai lambun zaitun, da shi da almajiransa suka shiga ciki.

2To, Yahuda, wanda ya bashe shi, ya san wurin, domin Yesu ya sha zuwa wurin da almajiransa. 3Saboda haka Yahuda ya zo cikin lambun, yana jagoranta ƙungiyar sojoji da waɗansu maʼaikata daga wurin manyan firistoci da Farisiyawa. Suna riƙe da toci, fitilu da kuma makamai.

4Yesu kuwa, sane da duk abin da zai same shi, ya fito ya tambaye, su ya ce, “Wa kuke nema?”

5Suka amsa suka ce, “Yesu Banazare.”

Yesu ya ce, “Ni ne.” (Yahuda kuwa wanda ya bashe shi yana nan tsaye tare da su.)
6Da Yesu ya ce, “Ni ne,” sai suka ja da baya suka fāɗi a ƙasa.

7Sai ya sāke tambayar su ya ce, “Wa kuke nema?”

Suka ce, “Yesu Banazare.”
8Yesu ya amsa, ya ce, “Ai, na gaya muku ni ne. In kuma ni ne kuke nema, sai ku bar waɗannan su tafi.” 9Wannan ya faru ne don a cika kalmomin da ya yi cewa: “Ban yar da ko ɗaya daga cikin waɗanda ka ba ni ba.”
Yoh 6.39


10Sai Siman Bitrus, wanda yake da takobi, ya zāre, ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama. (Sunan bawan kuwa Malkus ne.)

11Sai Yesu ya umarce Bitrus ya ce, “Mai da takobinka kube! Ba zan sha kwaf da Uba ya ba ni ba?”

An Kai Yesu a Gaban Annas

12Sai ƙungiyar soja tare da shugaban sojanta da kuma maʼaikatan Yahudawa suka kama Yesu. Suka ɗaure shi 13saʼan nan suka kawo shi da farko wurin Annas, wanda yake surukin Kayifas, babban firist a shekaran nan. 14Kayifas ne wanda ya shawarci Yahudawa cewa zai fi kyau mutum ɗaya yǎ mutu saboda mutane.

Mūsun Bitrus na Farko

15Siman Bitrus da kuma wani almajiri suna bin Yesu. Domin almajirin nan sananne ne ga babban firist, sai ya shiga tare da Yesu a filin gidan babban firist ɗin, 16Bitrus kuwa ya dakata a waje a bakin ƙofa. Almajirin nan da yake sananne ga babban firist, ya dawo ya yi magana da yarinyar mai aiki a can, ya kuma shigo da Bitrus.

17Yarinyar da take bakin ƙofar ta ce wa Bitrus, “Kai ba ɗaya ne daga cikin almajiran mutumin nan ba ne?”

Bitrus ya amsa, ya ce, “Aʼa, ba na ciki.”

18To, ana sanyi, bayi da maʼaikatan suna tsttsaye kewaye da wutan da suka hura don su ji ɗumi. Bitrus ma yana tsaye tare da su, yana jin ɗumi.

Babban Firist Ya Yi wa Yesu Tambayoyi

19Ana cikin haka, sai babban firist ya tuhumi Yesu game da almajiransa da kuma koyarwarsa.

20Yesu ya amsa, ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a fili. Na kuma sha yin koyarwa a majamiʼu ko kuma a haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban taɓa faɗin kome a ɓoye ba. 21Don me kake tuhumata? Ka tambayi waɗanda suka ji ni. Ba shakka, sun san abin da na faɗa.”

22Da Yesu ya faɗa haka, sai ɗaya daga cikin maʼaikatan da yake tsaye kusa ya mare shi a fuska ya ce, “Haka za ka amsa wa babban firist?”

23Yesu ya amsa, ya ce, “In na faɗi abin da ba daidai ba, ka nuna abin da ba daidai ba. Amma in gaskiya na faɗa, don me ka mare ni?” 24Sai Annas ya aika da shi, a ɗaure, wurin Kayifas babban firist.

Mūsun Bitrus na Biyu da na Uku

25Da Siman Bitrus yana nan tsaye yana jin ɗumin wuta, sai aka tambaye shi, “Kai, kai ma ba ɗaya daga cikin almajiransa ba ne?”

Sai ya yi mūsu, yana cewa, “Sam, ba na ciki.”
26Sai wani daga cikin bayin babban firist dangin wanda Bitrus ya sare wa kunne, ya tambaya shi ya ce, “Kana tsammani ban gan ka tare da shi a gonar zaitun ba?” 27Bitrus ya sāke yin mūsu, nan take kuwa zakara ya yi cara.

Yesu a Gaban Bilatus

28Saʼan nan Yahudawa suka fitar da Yesu daga wurin Kayifas zuwa fadar gwamnar Roma. A yanzu dai, safiya ta yi, don gudu kada su ƙazantar da kansu Yahudawa ba su shiga cikin fadar ba; sun so su iya ci Bikin Ƙetarewa. 29Saboda haka Bilatus ya fito wajensu ya ce, “Wace ƙara kuke kawowa game da mutumin nan?”

30Suka amsa suka ce, “Da a ce shi ba mai laifi ba ne, ai, da ba mu bashe shi gare ka ba.”

31Bilatus ya ce, “Ku tafi da shi da kanku mana, ku hukunta shi bisa ga dokarku.”

Sai Yahudawa suka ƙi suka ce, “Ba mu da ikon yanke wa wani hukuncin kisa.”
32Wannan kuwa ya faru ne don a cika kalmomin da Yesu ya yi da suka nuna irin mutuwar da zai yi.

33Sai Bilatus ya koma cikin fada, ya kira Yesu ya tambaye shi, “Shin, kai ne sarkin Yahudawa?”

34Yesu ya yi tambaya, ya ce, “Wannan raʼayin kanka ne, ko waɗansu ne suka yi maka magana game da ni?”

35Bilatus ya amsa, ya ce, “Ni Bayahude ne? Ai, mutanenka ne da kuma manyan firistoci suka bashe ka gare ni. Me ka yi?”

36Yesu ya ce, “Mulkina ba na duniyan nan ba ne. Da na duniyan nan ne da bayina sun yi yaƙi su hana Yahudawa kama ni. Amma fa mulkina daga wani waje ne.”

37Sai Bilatus ya ce, “To, wato, kai sarki ne!”

Yesu ya amsa, ya ce, “Haka yake, ni sarki ne yadda ka faɗa. Tabbatacce, saboda wannan dalili ne aka haife ni, kuma don wannan ne na zo duniya, domin in shaidi gaskiya. Duk wanda yake gefen gaskiya yakan saurare ni.”

38Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Mece ce gaskiya?” Da ya faɗi haka, sai ya sāke fitowa wurin Yahudawa ya ce, “Ni fa ban sami wani abin zargi game da shi ba. 39Amma fa kuna da wata alʼada in lokacin Bikin Ƙetarewa ya yi, nakan sakar muku da ɗan kurkuku ɗaya. To, kuna so in sakar muku ‘sarkin Yahudawa’?”

40Sai suka ɗau kururuwa suna cewa, “Kai, ba shi ba! A ba mu Barabbas!” To, Barabbas ɗin nan yana da hannu dumu-dumu a wani tawaye.

Copyright information for HauSRK